Za'a hana shan taba sigari a kasar Japan

Za'a hana shan taba sigari a kasar Japan

A karon farko kasar Japan ta amince da wata doka, wacce zata haramta wa kowane ma'aikacin gwamnati shan taba sigari

Za'a hana shan taba sigari a kasar Japan

Za'a hana shan taba sigari a kasar Japan

A karon farko kasar Japan ta amince da wata doka, wacce zata haramta wa kowane ma'aikacin gwamnati shan taba sigari, inda wuraren suka hada da asibitoci, makarantu, hukumomi da sauran wuraren ayyuka na gwamnati.

DUBA WANNAN: Ko kun san yawan hanyoyin da gwamnatin tarayya tayi daga shekarar data wuce zuwa yanzu

Amma dokar ta bawa kowacce ma'aikata ko hukumar bada izinin sha idan har akwai waje wanda yake da girman mita 100 a harabar wurin.

Abinda ya saka kasar ta saka dokar kuwa shine, domin rage yawan masu shan taba kafin lokacin gasar wasanni da tsalle - tsalle da za'ayi a birnin Tokyo a shekarar 2020. Dokar zata cigaba da zama har wannan lokaci.

Hasashe ya nuna cewa akwai mutane sama da miliyan 20 da suke shan taba sigari a kasar ta Japan wacce ke da kimanin yawan mutane miliyan 120.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel