Labarin wata 'yar Afirka data bar muhimmin tarihi a duniya

Labarin wata 'yar Afirka data bar muhimmin tarihi a duniya

- An haifi Huda Shaarawi a shekarar 1879 a Harem dake kasar Masar

- Harem wani wuri ne da ake kebewa Kwarkwarorin Sarki

Labarin wata 'yar Afirka data bar muhimmin tarihi a duniya
Labarin wata 'yar Afirka data bar muhimmin tarihi a duniya

An haifi Huda Shaarawi a shekarar 1879 a Harem dake kasar Masar. Harem wani wuri ne da ake kebewa Kwarkwarorin Sarki, galibin matan dake zama a Harem ba a basu damar zuwa makaranta, amma ita Huda tayi karatun ta a Harem. Sai dai kuma ta shiga damuwa bayan da ta fuskanci cewa ba a bata dama irin wacce aka ba 'yan'uwanta maza ba.

DUBA WANNAN: Kalli yawan kudaden da suke ajiye a Najeriya wanda har yanzu kotu bata bada damar a taba su ba

Ta ce: "Na shiga damuwa kuma na fara watsi da karatuna, na fara jin haushin kasancewata mace, kasancewata a cikin kwarkwarori ya hana ni neman ilimi, sannan kuma kasancewata 'ya mace ya hana ni 'yancin dana ke bukata."

Lokacin data kai shekara 13 a duniya, sai aka aurar da ita ga wani dan uwanta, wanda ya bata shekara 40. Ta ce ya zame mata wajibi ta amince domin kuwa bata da wani zabi da ya wuce hakan, ta ce ta yanke shawarar bayyana damuwarta da kuma yin bore.

A lokacin da ta girma sai ta fara shirya taruka, inda take saka mata su bayyana a gaban jama'a. Huda ta fara yin suna ne a lokacin data yi jifa da gyalenta a tashar jirgin kasa a birnin Alkhahira a shekarar 1923, inda ta bukaci sauran mata da suyi koyi abin da tayi.

Wannan shine karo na farko da aka nuna kyama ga gyale a bainar jama'a a kasar ta Masar, mata da yawa sunyi koyi da ita inda suka dinga cire gyalensu.

Huda ta kafa wata makarantar mata, sannan kuma ta kafa kungiyar fafutikar kwato hakkin mata, dalilin haka aka kara yawan shekarun aurar da mata zuwa shekara 16 bayan ta jagoranci neman bukatar hakan.

Huda ta rasu ne a shekarar 1947 bayan ta shafe lokaci tana gwagwarmayar kare hakkin mata da yara.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng