Kasar China za ta inganta harkar wuta a kasar nan – Gwamnatin Buhari
Labari ya iso gare mu cewa Gwamnatin Kasar China za ta inganta harkar wuta a Najeriya. Gwamnatin Tarayyar ce dai ta bayyan wannan ta bakin Ministan kimiyya da fasaha Dr. Ogbonnaya Onu.
A wajen wani taron bita da aka shirya game da harkar samar da wutan lantarki ta ruwa, Ministan kasar Ogbonnaya Onu ya bayyanawa jam’a cewa China ta shirya taimakawa kasar nan ta samu wutan da zai kai karfin megawatt 19, 000.
Kamar yadda mu ka samu labari Bitrus Nabasu wanda babban Sakatare ne a Ma’aikatar kimiyya da fasahar kasar ya wakilci Ministan a wajen wannan taro da Mutanen Kasar China su ka shirya jiya Talata a babban Birnin Tarayya Abuja.
KU KARANTA: An jinjinawa Shugaba Buhari na dawo da kamfanin jirgin saman Najeriya
An dai shirya taron ne domin ganin yadda za a inganta lantarki a Najeriya. Zhao Linxiang, wani babban Jami’in Kasar ta Sin watau China a Najeriya yace wannan ne karo na farko da aka shirya irin wannan taro a Gwamnatin Shugaba Buhari.
Linxiang ya koka da matsalar wutan da ake fama da ita nda yace Najeriya na da arzikin da za tayi maganin wahalar lantarki ganin yadda ake da ruwa. Idan wutan kasra ta karu zuwa megawatt 19,000 dai ana iya cewa za a rage ganin duhu.
Kwanaki kun ji labari cewa Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewa za a samu karuwar wutan lantarki a kasar nan da zuwa badi war haka inda ake kokarin a tada wasu tashohin wuta na kasar a wasu Jihohi da dama.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng