Kwarto da farkarsa sun shiga hannu, bayan da makwabta suka sanya kwado ta waje suka kulle su kwana daya

Kwarto da farkarsa sun shiga hannu, bayan da makwabta suka sanya kwado ta waje suka kulle su kwana daya

- Ya dade yana zuwa gidan ashe makwabta sun sa masa ido

- Maigidan kanyi tafiya ya dade

- Sai da safe aka fiddo su aka kai wa 'yansanda

Kwarto da farkarsa sun shiga hannu, bayan da makwabta suka sanya kwado ta waje suka kulle su kwana daya
Kwarto da farkarsa sun shiga hannu, bayan da makwabta suka sanya kwado ta waje suka kulle su kwana daya

A Harare, babban birnin Zimbabwe, a wani kauye mai suna Chinotimba, wasu makwabta, sun kulle gidan makwabcinsu, bayan da suka tabbatar Godfrey Makeche Ncube mai gida yazo ya kama Tafireyi Zimba masoyin matarsa Cynthia Ngwenya.

A cikin darre kauyawan suka fakaice su suka kulle su ta waje, har zuwa safiya, inda da gari ya waye suka yi holinsu a kauyen, kafin daga bisani, su aika su ofishin 'yansanda domin fuskantar hukunci.

DUBA WANNAN: Tsokacin Sheikh Dahiru Bauchi kan kashe-kashe

A dokar kasar dai dai, sai dai a raba auren na iyalan, amma babu wani hukuncin doka da ya nuna masoyan sun yi laifi, sai dai fa ko in akwai cin zarafi da bata suna. Yansanda ma sun hana shi maigidan bada bahasi ga 'yan jarida kan batun.

Da aka tambaye shi, maigidan yace baya son cewa komi, ganin ma yanzu haka suna da jariri dan wata shida da suke raino.

Aiki ne dai ya kaishi wani kauyen inda yakan shafe dare yana aikin gadi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng