Mugun gani: Wani Uba ya kama Ɗansa turmi da taɓarya yana luwaɗi da karamin yaro a Kaduna
Allah wadaran naka ya lalace, wai inji jakin dawa ya ci kari da jakin gida, wannan shine kwatankwacin abinda ya faru a jihar Kaduna, inda dubun wani dalibin jami’ar jihar Kaduna, KASU, mai shekaru 18 dake aikata luwadi, mai suna Muhammad ta cika.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito mahaifin wannan yaro ne ya kama shi turmi da tabarya da wani karamin yaro a gidansu dake unguwar hayin dan bushiya na jihar Kaduna, inda ya garzaya da shi zuwa ofishin yan kato da gora na unguwar, kuma ya mika shi ga jami’an.
KU KARANTA: Yan bindiga sun yi garkuwa da wani Basarake a Lokoja, sun bindige Dansa
Da ake zantawa da Muhammad, ya bayyana cewa yana yin luwadi ne ba don sha’awa ba, sai dai don ya samu budin kwakwalwa da karin fahimta, tare da samun ilimi, musamman saboda dalibin jami’a ne shi, kuma ba shi da kokari.
Sai dai ya tabbatar da cewar tabbas tun bayan da ya fara wannan mummunan dabi’a yana samun karin fahimtar karatunsa, kuma yana samun sakamakon da yake bukata, amma ya kara da cewa suna amfani da aljanu wajen wannan tsafe tsafe.
Bugu da kari dalibin ya bayyana cewa suna daywa dake cikin wannan kungiya a Najeriya, kuma suna da shaida da ake yi ma kowa a kafadarsa, har ma ya nuna ma manema labaru nasa shaidar, kuma yace suna ganawa ne ta cikin ruhi ko ta cikin mafarki, ta nan ne aka kara musu karfin ruhi.
Sai dai daga karshe wannan dalibi ya yi da na sanin abinda ya aikata, tare da yin nadamar halin da ya tsinci kansa a ciki, inda ya bayyana cewa yana tsoron fushin Allah, tare da kunyar iyayensa.
A nan sai dai mu ce Allah ya shiryemu gaba daya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng