Zaben 2019: Mutanen da ke harin kujerar Sanata Kwankwaso a Kano

Zaben 2019: Mutanen da ke harin kujerar Sanata Kwankwaso a Kano

Mun fahimci cewa an samu wasu da ke hangen kujerar Sanatan Kano ta tsakiya wanda yanzu tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso yake kai. A tarihin Kano dai babu wanda ya taba zarcewa a kan wannan kujerar.

Zaben 2019: Mutanen da ke harin kujerar Sanata Kwankwaso a Kano
Kujerar Kwankwaso a Kano tana rawa bayan rikicin sa da Ganduje

Daga cikin masu neman kujerar Sanatan na tsakiyar Kano akwai:

1. Bashir Lado

Rabiu Kwankwaso ya tika Sanata Bashir Lado ne a zaben 2015. Kuma yanzu tsohon Sanatan ya dawo APC inda ake tunanin Gwamna zai ba shi tikiti domin komawa kujerar sa a maimakon Kwankwaso.

2. Nasiru Yusuf Gawuna

Dr. Nasiru Gawuna yana cikin masu neman kujerar Sanatan Kano ta tsakiya. Gawuna tsohon Kwamishinan Kwankwaso ne kuma har yanzu Ganduje na damawa da shi kwarai da gaske.

KU KARANTA: Kashi 90% na Mutanen Kwara za su zabi Shugaban Kasa Buhari a 2019

3. Ibrahim Shekarau

Babu mamaki tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau ya fito kujerar Sanata a Kano. Shekarau dai zai nemi ya sake takarar Shugaban kasa a karkashin PDP, sai dai ba dole bane ya iya kai labari a nan.

4. Ibrahim Kankarofi

Ibrahim Kankarofi wani rikakken ‘Dan siyasa ne kuma tsohon Ma’aikacin Gwamnatin Kano. Kankarofi yana cikin manyan Sakatarorin Gwamnatin Ganduje kuma zai nemi doke Kwankwaso a 2019.

5. Garba Yusuf

Babu mamaki tsohon Kwamishinan Jihar a karkashin Gwamnatin ANPP ya fito takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya. Ana rade-radin Garba Izala na cikin masu dakon kujerar ta Kwankwaso.

6. Ghali Umar Na’abba

Ba za ayi mamaki idan Tsohon Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya ya jarraba sa’ar sa ba a 2019. Tsohon ‘Dan Majalisar ya taba neman takaran Sanata lokacin yana PDP amma ya sha kasa tun kafin a kai ko ina.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng