An cuci bakauye: Yan damfara sun samar da wata bishiya da ake bautamawa a Kano (Hotuna)

An cuci bakauye: Yan damfara sun samar da wata bishiya da ake bautamawa a Kano (Hotuna)

Kaico, abin mamaki baya karewa, kamar yadda Annabin Allah ya tabbatar dayake cewa, duk wanda yayi tsawon rai zai ga sabani daban daban, kwatankwacin haka ne ya faru a jihar Kano, inda duk da wadatar ilimi na wannan zamani, amma sai ga wasu mutane suna bautar bishiya.

Legit.ng ta ruwaito Hukumar Hisbah ta jihar Kano, wanda aka fi sani da A daidaita sahu ta samu nasarar kawar da wata mummunar dabi’a dake faruwa a jihar Kano, inda aka samu wani sashi na al’ummar Kano suna bautama wata bishiya.

KU KARANTA: Manyan abubuwa guda 8 dake kawo mutuwar aure daga bangaren Miji

An cuci bakauye: Yan damfara sun samar da wata bishiya da ake bautamawa a Kano (Hotuna)
Bishiyar

Wannan lamari ya faru ne a wani kauye dake cikin karamar hukumar Kunchi na jihar Kano, inda ake zaton wasu yan damfara sun zana hoton Ka’aba, Tauraro da kuma Allo a jikin wani bishiya, inda su kuma mazauna kauyen suka mayar da bishiyar abin bauta, suna biyan kudi suna zuwan bauta a wajen.

Sai dai jami’an hukumar Hisbah sun yi ta maza, inda su lallaba cikin dare suka sassare wannan bishiya, tare da yi ma gunduwa gunduwa, bayan an kai ruwa rana tsakanin hukumar da yan damafarar, sakamakon suna samun makudan kudade.

An cuci bakauye: Yan damfara sun samar da wata bishiya da ake bautamawa a Kano (Hotuna)
Bishiyar

Da wannan ne hukumar take kira ga Malamana addinin Musulunci da su dinga shiga kauyuka da lunguna a garuruwan Musulmai don yada sahihin da’awar addinin Musulunci don wayar da kawunan jama’a daga duhun jahilci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: