Mai kamfanin Amazon Jeff Bezos ya ba Dala Biliyan 150 baya

Mai kamfanin Amazon Jeff Bezos ya ba Dala Biliyan 150 baya

Jeff Bezos ya kafa tarihi inda ya zama wanda ya fi kowa mallakar dukiya a tarihin Duniya. Bezos shi ne Mai kamfanin nan na Amazon. A bana dai ya kerewa Bill Gates a sahun masu kudin Duniya.

Mai kamfanin Amazon Jeff Bezos ya ba Dala Biliyan 150 baya
Shugaban kamfanin nan na Amazon watau Jeff Bezos

Yanzu dai Jeff Bezos ya ba Dala Biliyan 150 baya kamar yadda Jaridar Bloomberg ta kasar waje ta bayyana. Hakan na nufin Bezos ya zarce Bill Gates dukiya da kusan Dala Biliyan 55. Bill Gates shi ne wanda ya fi kowa kudi a da.

Shugaban Kamfanin na Amazon Jeff Bezos mai shekaru 54 a Duniya ya mallaki abin da ya haura Dala Biliyan 100 wanda Bill Gates ya taba mallaka a shekarar 1999. Tun wancan lokaci ake ji da Mista Bill Gates cikin Attajiran Duniya.

KU KARANTA:

A kusan shekara guda dai Bezos ya samu sama da Dala Biliyan 52. Wannan makudan kudi dai sun fi gaba daya abin da mai kudin Nahiyar Asiya. A tarihin Duniya dai ba a taba ganin mutumin da ya mallaki wannan makudin kudi ba.

Mai kudin nan Bill Gates wanda shi ne Shugaban Kamfanin Microsoft ne na biyu a Duniya inda yake da kusan Dala Biliyan 100. Warren Buffet kuma ne na uku a jerin Attajiran Duniya inda shi kuma ya ba Dala Biliyan 83.

Tun shekaru 23 da suka wuce Bill Gates yake cikin Attajiran Duniya. Yanzu dai an samu wani Attajirin da ya sha gaban Mista Bill Gates. Bill Gates ya mallaki kudin sa ne ta harkar komfuta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel