Jam’iyyar APC tayi asarar manyan ‘Yan siyasa a rana daya

Jam’iyyar APC tayi asarar manyan ‘Yan siyasa a rana daya

- APC ta sake yin rashi yayin da Sanata Nyako ya tsere daga Jam’iyyar yau

- Jam’iyyar ta rasa wani ‘Dan Majalisa kuma zuwa Jam’iyyar adawa ADC

- Wani na kusa da Shugaban Majalisar Dattawa Saraki ma yayi ficewar sa

Jam’iyyar APC tayi asarar manyan ‘Yan siyasa a rana daya
Gwamnan Jihar Benuwai Ortom ya tsere daga APC

1. Samuel Ortom

Jam’iyyar APC ta gamu da asara a Yankin Arewa ta tsakiya bayan ficewar Gwamna Ortom na Jihar Benuwai. Gwamna Ortom ya bayyana cewa yanzu an ba sa jan kati daga Jam’iyyar APC mai mulki.

KU KARANTA: Gwamnan Benuwai Ortom ya bar APC yau

2. Abdulaziz Nyako

Mun samu labari ba da dadewa yau dinnan cewa Sanatan da ke wakiltar Adamawa ta tsakiya a Majalisar Dattawa watau Abdulaziz Nyako ya fice daga Jam’iyyar ta APC mai mulkin Kasar nan.

3. Rafiu Umar

Wani ‘Dan Majalisa da ke wakiltar Yankin Gombi a Majalisar dokokin Jihar Rafiu Umar ya tsere tare da shi. Shi ma Hon. Rafiu Umar ya koka da cewa ba ayi masa adalci sam a Jam’iyyar APC mai mulki.

4. Usman Bawa

Wani mai ba Shugaban Majalisar Wakilai na Tarayya Yakubu Dogara ya bar Jam’iyyar. Usman Bawa wanda tsohon ‘Dan Majalisa ne ya bar Jam’iyyar APC kamar yadda wani Hadimin Shugaban Majalisar ya fada.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng