Shugaba Buhari ya yaba da ingancin kwarewar yan Najeriya a fannin ayyuka daban-daban a kasar Netherlands

Shugaba Buhari ya yaba da ingancin kwarewar yan Najeriya a fannin ayyuka daban-daban a kasar Netherlands

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna farin ciki da jin dadi kan yadda ya samu mutanen kasarsa Najeriya cike da kwarewa a kas Netherlands.

Shugaban kasar ya gana da mambobin kungiyar yan Najeriya a kasar waje, reshen kasar Netherlands, a ranar Litinin, 16 ga watan Yuli a ziyarar aiki da ya kai Hague, Netherlands.

Ya yiwa mutanen kasar nasa fatan akhairi a fannin ayyukansu daban-daban inda ya nuna jin dadinsa akan jajircewarsu.

Shugaba Buhari ya yaba da ingancin kwarewar yan Najeriya fannin ayyuka daban-daban a kasar Netherlands

Shugaba Buhari ya yaba da ingancin kwarewar yan Najeriya fannin ayyuka daban-daban a kasar Netherlands

Ya ce: “Na ji dadin irin kwararrun mutane da nake gani. Lallai kuna da tarin inganci. Ina taya ku murna kan nasarorin da kuka samu.”

KU KARANTA KUMA: Bana tsoron EFCC, ba zan gudu na bar Najeriya ba - Fayose

Ya yaba masu kan yadda suka daukaka martabar kasarsu Najeriya da kuma kasancewa tare da kasar a chan inda suke.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa kasar Netherland da misalin karfe 7:23 na yammacin Lahadi, 16 ga watan Yuli, don halartar taron Kotun Duniya, ICC, a birnin Hague na kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel