Yadda wani Magidanci ya halaka Uwargidarsa bayan ya kamata tana kwartanci

Yadda wani Magidanci ya halaka Uwargidarsa bayan ya kamata tana kwartanci

Jami’an rundunar Yansandan jihar Neja sun samu nasarar cafke wani matashin Magidanci mai shekaru 25, Bello Muhe, da laifin yi ma uwargidarsa kisan gilla, bayan ya yi yunkurin tserewa, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Muhe dan asalin kauyen Gautan Fadama ne, dake cikin karamar hukumar Bagudo na jihar Kebbi, inda ya hallaka Matarsa mai shekaru ashirin da biyar, kan zarginta da kwartanci, wanda hakan ya sanya Muhe turata gidan iyayenta, amma ta cigaba da bin maza a can, a cewarsa.

KU KARANTA: Horo mai tsanani: Babban laifin da gwamnatin PDP ta tafka ma jama’an jihar Ekiti

Yadda wani Magidanci ya halaka Uwargidarsa bayan ya kamata tana kwartanci
Magidanci

Sai dai wannan mummunan dabi’a da Muhe ke zargin matarsa da shi ya cigaba da kona masa rai, inda ya hau dokin zuciya ya aikata mata aika aika. “Na yi amfani ne da adda wajen kasheta, sakamakon duk kokarin da na yin a ganin ta daina bin maza ya gagara, na yi mata magana ta ki ki.” Inji shi.

Muhe ya cigaba da fadin; “Matata na tsananin taurin kai, na sha zaunar da ita na ja mata kunne game da halayyatar na bin maza, amma ta ki ta daina, ta yi kunnen uwar shegu, wannan ya sa dole ta dandana kudarta.”

A nata bangare, rundunar Yansandan jihar, ta bakin Kaakakinta, Muhammad Abubakar ta bayyana cewa tuni ta gurfanar da Muhe gaban kuliya manta sabo don yanke masa hukuncin da ya dace.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: