2019: Nasarar APC a Ekiti zai maimata kansa a kudu maso gabas – Magoya bayan Buhari

2019: Nasarar APC a Ekiti zai maimata kansa a kudu maso gabas – Magoya bayan Buhari

Wasu masu biyyaya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari karkashin kungiyar Buhari Support Organisation, reshen jihar Enugu a ranar Lahadi, 15 ga watan Yuli sunyi has ashen cewa nasarar jam’iyyar All Progressives Congress a zaben gwamna da aka yi a jihar Ekiti zai maimaita kansa a kudu maso gabas a 2019.

Kungiyar BSO, jihar Enugu tayi wannan hasashe ne sakon taya murna ga Kayode Fayemi, gwamnan jihar Ekiti mai jiran gado, kan nasarar da yayi a zaben ranar Asabar.

2019: Nasarar APC a Ekiti zai maimata kansa a kudu maso gabas – Magoya bayan Buhari

2019: Nasarar APC a Ekiti zai maimata kansa a kudu maso gabas – Magoya bayan Buhari
Source: Depositphotos

Fayemi, dan takarar APC kuma tsohon ministan ma’adinai ya samu kuri’u 197,459 inda ya kayar da babban abokin takararsa, Farfesa Olusola Eleka na jam’iyyar Peoples Democratic Party, wadda ya samu 178,121.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar APC ta fara harin Taraba da Gombe bayan lashe zaben Ekiti Jam’iyyar APC ta fara harin Taraba da Gombe bayan lashe zaben Ekiti

Da yake martani akan nasarar a sakon taya murna a ranar Lahadi, Godwin Onwusi, sakataren kungiyar reshen Enugu, ya yabi mutanen Ekiti da suka zabi Fayemi.

A zaben 2014, PDP ce tayi nasara a Ekiti, sai dai kuma ta fadi zaben Shugaban kasa. Yanzu dai a zabukan Gwamnoni da aka yi bayan 2015, PDP ta iya lashe Bayelsa ne kurum inda ta sha kasa a Kogi, Ondo, Edo da kuma Ekiti a yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel