Sama da mutane 1,500 suka canja sheka daga PDP suka koma APC
Sama da mutum 1,500 ne suka canja sheka daga babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) suka koma jam'iyya mai ci ta yanzu wato All Progressives Congress (APC) a karamar hukumar Abaji
Sama da mutum 1,500 ne suka canja sheka daga babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) suka koma jam'iyya mai ci ta yanzu wato All Progressives Congress (APC) a karamar hukumar Abaji.
Manya daga cikin wadanda suka canja shekan, sun hada da tsohon daraktan yawon kamfen na karamar hukumar, Alhaji Muhammad Angulu Bello; sai mataimakin ma'aji na jam'iyyar PDP, Salihu Musa Soje; jigo a jam'iyyar PDP, Hajiya Ramatu Danjuma; sai mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na yankin, Adamu Danjuma Ozuye; da dai sauran manya a jam'iyyar ta PDP.
DUBA WANNAN: Wasu alkawurra da sabon Gwamnan Ekiti ya yiwa al'ummar jihar
Shugaban jam'iyyar APC na yankin, Alhaji Mohammed Haruna Yaba, wanda ya karbi masu canja shekar wanda aka gabatar a dakin taro na Adamu Shu'aibu Memorial Town Hall, a ranar Asabar dinnan data gabata, shugaban ya tabbatar musu da cewar sunyi tunani mai kyau na dawowa jam'iyyar APC.
Ya kuma tabbatar musu da cewa jam'iyyar APC zata dauke su babu bambanci da kowa, sannan zata basu dama domin bada gudunmawar su ga jam'iyyar, sannan kuma ya bukaci 'yan jam'iyyar PDP da suyi koyi da wadanda suka canja shekar a yanzu.
Mai magana da yawun masu canja shekar, tsohon shugaban jam'iyyar PDP na yankin, Adamu Danjuma Ozuye, yace sun yanke hukuncin barin jam'iyyar ta PDP ne saboda ganin irin rashin cigaba da ake samu a jam'iyyar musamman ma a karkashin mulkin sabon shugaban jam'iyyar na yankin a yanzu, Alhaji Abdulrahman Ajiya.
Ya ce irin cigaban da jam'iyyar APC ta kawo a karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba karami bane a kasar nan.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng