Ina dalili: Babu abin da zai sa in taya Fayemi murnar lashe zabe – Ayo Fayose

Ina dalili: Babu abin da zai sa in taya Fayemi murnar lashe zabe – Ayo Fayose

- Gwamna Jihar Ekiti yace ba zai taya Fayemi murnar lashe zabe ba

- Ayodele Fayose na PDP yace ba shi Jam’iyyar APC ta tika da kasa ba

- Gwamnan yace Farfesa Olusola Eleka ne ‘Dan takarar Jam’iyyar PDP

Jiya labari ya zo mana cewa Gwamnan Jihar Ekiti wanda ke shirin barin gado watau Ayo Fayose yace babu abin da zai sa ya taya ‘Dan takarar APC Kayode Fayemi da yayi nasara a zaben murna.

Ina dalili: Babu abin da zai sa in taya Fayemi murnar lashe zabe – Ayo Fayose
Gwamna Ayo Fayose yace ba zai taya Kayode Fayemi murna ba

Channels TV ta rahoto Gwamna Ayodele Fayose wanda Mataimakin sa ne yayi takara a karkashin Jam’iyyar PDP yana cewa sam bai ga dalilin yi wa Abokin gaban na sa murna ba don kuwa ba da shi aka yi takara ba.

Kamar yadda gidan Talabijin ta rahoto, Gwamna Fayose yace ‘Dan takarar PDP Farfesa Olusola Eleka ne ya kamata ya kira Fayemi don da shi su gwabza takara. Fayose yace shi babu sunan sa cikin masu takara.

KU KARANTA: PDP tayi watsi da sakamakon zaben Ekiti

Jama’a sun jira su ji ko Gwamnan zai yi irin abin da aka yi masa a 2014 lokacin da ya lashe zaben Gwamna. Fayemi a lokacin yana Gwamna ya kira Fayose a waya, ya taya sa murna duk da kashin da ya sha a zaben.

Shi dai Ayo Fayose wanda ya sha kunya a zaben da aka yi a karshen makon nan yace ba shi APC ta tika da kasa ba. Tsohon Ministan Buhari watau Kayode Fayemi ne ya lashe zaben da aka gudanar inda ya doke PDP.

Tuni dai irin su Shugaban Kasa Buhari da Mai dakin sa Aisha Buhari, da ma Bukola Saraki, da Olusegun Obasanjo da sauran manyan Kasar su ka taya sabon Gwamnan murna na komawa kujerar sa da ya rasa a 2014.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel