Mataimakin Shugaban Kasa yace bai da wanda yake da ita a Duniya irin Mai dakin sa
- Jiya ne ranar zagayowar haihuwar mai dakin Yemi Osinbajo
- Farfesa Yemi Osinbajo ya nuna yadda yake kaunar matar sa
- Osinbajo yace Sahibar ta sa tana nan da kyawun ta kamar da
A jiya ne Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya taya matar sa murnar zagayowar Ranar haihuwar ta inda ya bayyana yadda soyayyar su ta fara tun su na ‘Yan samari. Dolapo Jikar Marigayi Obafemi Awolowo ce.
Yemi Osinbajo ya bayyana cewa shekarun baya ne ya hadu da Oludolapo wanda bayan sun fahimci juna ta zama Sahibar sa. Mataimakin Shugaban kasar yace a yanzu bai da kamar Uwar ‘Ya ‘yan ta sa a kaf fadin Duniyar nan.
KU KARANTA: An nemi a ga bayan wani Gwamnan APC a Arewa
Osinbajo SAN ya kuma bayyana cewa Mai dakin ta sa tana nan da kyawun ta da ya san ta da shi tun lokacin da su ka fara haduwa a baya. Tun a shekarar 1989 ne Osinbajo ya auri Mai dakin ta sa lokacin yana Malamin Makaranta.
Mataimakin Shugaban na Najeriya Farfesa Osinbajo yace Mai dakin ta sa ita ce jiyan sa, kuma ita ce yau da gobe sa. Farfesan ya nuna cewa Matar ta sa ita ce bangon da ta rike sa. Osinbajo ya kara da cewa zuciyar ta ne wurin zaman sa.
Yanzu haka dai Mataimakin Shugaban Kasar sun haifi ‘Ya ‘ya 3 da Mai dakin ta sa wanda a ciki har guda tayi aure a bana. Osinbajo ya aikawa Matar ta sa wannan sako ne a shafin sa na sadarwa na zamani domin taya ta murna a jiya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng