An binne mutane 32 da yan fashi suka kashe a Sokoto (hoto)
Anyi jana’izzar mutane da yawa a kauyen Tabbannin Gera dake Sokoto bayan yan fashi sun kashe mutane 32 a kauyuka hudu na jihohin Sokoto da Zamfara.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ba iyalan wadanda abun ya cika da su tabbacin daukar mataki a Rabah domin magance matsalar da kuma tabbatar da sun koma kauyukansu.
Gwamnatin jihar ta kuma rarraba kayan agaji na miliyoyin naira ga wadanda abun ya shafa.
An tattaro cewa yan fashin sun kai farmaki kauyukan da Babura sama da 100 da misalin karfe 3pm na rana ionda suke ta harbin mutanen da suka gani.
KU KARANTA KUMA: Buhari ya yi Allah wadai da harin jihar Sokoto, ya sha alwashin kare yan Najeriya
Kauyukan da abun ya shafa sun hada da Alliki, Birwanga, Tabbannin Gera a karamar hukumar Gera dake jihar Sokoto da kuma kauyen Kozi a karamar hukumar Maradun dake jihar Zamfara.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng