Duk da arzikin fetur: Najeriya ce sahun gaba a jerin matsiyatan kasashe

Duk da arzikin fetur: Najeriya ce sahun gaba a jerin matsiyatan kasashe

Yanzu dai duk Duniya babu kasar da ta kai Najeriya tarin matsiyata duk da arzikin man fetur da Allah ya ba kasar. Bincike ya nuna cewa Najeriya ta kerewa kasar Indiya wajen yawan masu fama da talauci.

Duk da arzikin fetur: Najeriya ce sahun gaba a jerin matsiyatan kasashe
Ana fama da mugun talauci har a cikin Yankin Neja Delta mai arzikin fetur

Alkaluman da Brookings Institution ta fitar kwanaki sun tabbatar da cewa yanzu haka akwai Talakawa na gidi har kusan Miliyan 90 a Najeriya. A Indiya dai Talakawa ba su kai Miliyan 75 ba duk da cewa Indiya ta fi Najeriya yawan jama’a.

Bugu da kari kuma Allah yayi wa Najeriya arzikin man fetur wanda bai yi wa kasar amfanin da ya kamata ba. Ana harsahen cewa Najeriya ta samu abin da ya kusa kai Dala Biliyan 500 ta hanyar man fetur a cikin shekaru 10 da su ka wuce.

KU KARANTA: An ba ‘Yan Sanda umarni su sassabe teba ko a kore su daga aiki a Indiya

Najeriya dai ba tayi aikin da ya kamata da wadannan kudi ba inda ake fama da rashin abubuwan more rayuwa inji Jaridar Zero Hedge. A Indiya dai ana samun raguwar talauci ne yayin da a nan Najeriya kuwa abin gaba yake kara yi kullum.

A duk minti guda sai an samu mutane 6 da su ka zama Matsiyata a Najeriya kamar yadda alkaluma su ka nuna. A Indiya akwai mutum sama da Biliyan 1 inda kuma Najeriya ake fama da kasa da mutum miliyan 200 a yanzu da mu ke magana.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ya dage wajen yunkurin sa na zama Shugaban kasa a 2019. Kwanaki Atiku ya je Landan ya bayyana yadda zai kawo karshen talauci a Najeriya idan har ya samu mulkin kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng