Zaben jihar Ekiti: ‘Yan sanda sun kama wasu ‘yan PDP da dangwalallun kuri’un zabe

Zaben jihar Ekiti: ‘Yan sanda sun kama wasu ‘yan PDP da dangwalallun kuri’un zabe

Yayin day a rage saura kwanaki hudu a yi zaben gwamna a Ekiti, hukumar ‘yan sanda a jihar ta kama wasu ‘yan jam’iyyar PDP da kuri’un da aka kamala dangwale su. Dukkan kuri’un an dangwalawa PDP ne.

A wani rahoto da Mista Wole Olujobi, Darektan yada labarai na kamfen din Kayode Fayemi, dan takarar APC, ya fitar ya bayyana sunayen mutane biyun da aka kama; Ashiru Gbenga da Olaide Olayeye.

Yanzu haka suna bawa jami’an ‘yan sanda muhimman bayanai dangane da kuri’un da aka kama su da su.

Zaben jihar Ekiti: ‘Yan sanda sun kama wasu ‘yan PDP da dangwalallun kuri’un zabe

Zaben jihar Ekiti: ‘Yan sanda sun kama wasu ‘yan PDP da dangwalallun kuri’un zabe

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Ekiti, Mista Caleb Ikechukwu, ya yi alkawarin samar da Karin bayani ga jaridar The Nation bayan sun nemi jin ta bakinsa a kan lamarin.

DUBA WANNAN: Tsiyar Nasarar: Sanata, dan majalisar wakilai da bulaliyar majalisa a jihar Fayose sun koma APC

Rahotanni sun bayyana cewar da misalign karfe 12:00 na rana ne aka sanar da hukumar ‘yan sanda ganin wata mota kirar Vien Foton mai dauke da lamba KTU 477 DG da ta zo daga Legas a ajiye a kasuwar Fayose dake kan titin Ajilosun a Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.

Zargin wurin da aka ga motar ne ya saka jami’an ‘yan sanda suka fara bincikenta kuma daga bisani suka gano kuri’un da aka zo da su a dangwale a cikin motar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel