Harkar tsaro: Jami’an tsaro a Indiya za su bar aiki idan ba su rage kiba ba

Harkar tsaro: Jami’an tsaro a Indiya za su bar aiki idan ba su rage kiba ba

Mun samu labari daga Jaridar Independent ta Turai cewa Jami’an ‘Yan Sanda a kasar Indiya za su ga ta kan su bayan da manyan su su ka ba su umarni su rage teba ko kuma a dakatar da su ko a kore su daga aiki a Kasar gaba daya.

Manyan Jami’an tsaro na kasar Indiya sun nemi ‘Yan Sanda su rage katon ciki da teba ko kuma a dakatar da su daga aiki. Nauyin da Jami’an tsaron ke yi ya na hana su aiki yadda ya kamata kamar yadda mu ka samu labari.

Shugaban ‘Yan Sandan Yankin Karnataka na kasar Indiya ya koka da yadda manyan ‘Yan Sanda su kayi ‘dan-karen nauyi a Yankin. Babban Jami’in ‘Yan Sandan Kasar Bhaskar Rao ya koka da halin da ‘Yan Sandan ke ciki.

KU KARANTA: Sanatocin Najeriya za su kuma takawa Shugaban kasa Buhari burki

Rao ya bayyana wannan ne bayan da ya fahimci cewa ‘Yan Sanda da dama sun mutu a dalilin shaye-shaye na giya da sauran kayan maye. Yawan shan giya da kuma rashin atasaye ne yayi sanadiyyar kiban ‘Yan Sandan.

Manyan ‘Yan Sandan sun bada wannan doka ne bayan da sama da ‘Yan Sanda 100 su ka mutu a dalilin nauyi da su kayi a shekarar nan. Za a dakatar da ‘Yan Sandan da su ka gaza rage teba wanda bayan nan za a kore wanda ya saba.

Dazu kun samu labari cewa Jakadar Najeriya zuwa Jamhuriyyar Sao Tome and Principe ta rasu shekaran jiya. Queen Worlu ta cika ne a Ranar 9 ga watan nan ta na bakin aikin ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel