Zaben Ekiti: Shugaban kasa Buhari ya ba marada kunya a Jihar Ekiti

Zaben Ekiti: Shugaban kasa Buhari ya ba marada kunya a Jihar Ekiti

Hausawa na cewa Zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi. A jiya ne dai Shugaba Buhari ya shiga Jihar Ekiti domin yi wa ‘Dan takarar Gwamnan APC Kayode Fayemi kamfe na zaben da za ayi a karshen makon nan.

Zaben Ekiti: Shugaban kasa Buhari ya ba marada kunya a Jihar Ekiti
Buhari ya tara jama’a a Ekiti duk da ‘danyen shirin Fayose

Kafin nan mun ji cewa Ayo Fayose yayi ta kokarin hana Shugaba Buhari shigowa cikin Garin na Ekiti. Gwamna Fayose ya hana motocin haya yawo a Jihar domin ganin an kawowa magoya bayan Jam’iyyar APC cikas wajen taron na jiya.

Sai dai wannan shiri da Gwamnan yayi bai kai ko ina ba ganin irin yadda dinbin Jama’a su ka fito zuwa filin wasa na Oluyemi Kayode da ke Garin Ado-Ekiti a cikin Jihar inda Shugaba Buhari da manyan APC su kayi taron yakin neman zaben.

Wasu ma dai na cewa Gwamna Ayo Fayose wanda rikakken 'Dan adawar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne bai biya masu motocin kudi kamar yadda yayi masu alkawarin ba. Wannan dai ya jawowa Gwamnan mai shirin barin gado suka.

KU KARANTA: An damke kamfanin Fayose su na buga takardun zaben bogi

Ana cewa Ayo Fayose ya rufe motocin haya ne a gidan Gwamnati da kuma ofisoshin Kananan Hukuma domin hana zirga-zirgar Jama’a lokacin da Shugaban kasar ya zo. Gwamnan yayi alkawarin biyan masu motocin kudi don su yi hakan.

Gwamna Fayose dai ya saduda daga baya inda ya nemi Shugaban kasar ya bar masa Jiha bayen kamfe. Bayan nan dai wasu Magoya bayan Shugaban kasa Buhari sun yi gangami a Birnin Tarayya domin nuna goyon bayan su ga Shugaban.

Jiya kun samu labari cewa daya daga cikin Ministocin Shugaban kasa Muhammadu Buhari watau Sanata Chris Ngige yayi tuntuben harshe inda ya nemi Jama’an Ekiti su zabi Ayodele Fayose na Jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel