Saurayi dan shekara 34 wanda yake na 3 a jerin masu kudin duniya

Saurayi dan shekara 34 wanda yake na 3 a jerin masu kudin duniya

Mark Zuckerberg, yanzu shine mai kudi na uku a duniya, inda ya sha gaban Warren Buffett a jerin da jaridar Bloomberg ta rubuto na manyan masu kudin duniya

Duniya gidan kashe ahu: Ku duba kuga mutum na 3 a jerin masu kudin duniya

Duniya gidan kashe ahu: Ku duba kuga mutum na 3 a jerin masu kudin duniya

Mark Zuckerberg, yanzu shine mai kudi na uku a duniya, inda ya sha gaban Warren Buffett a jerin da jaridar Bloomberg ta rubuto na manyan masu kudin duniya.

Zuckerberg ya wuce Buffett a yayin da hannun jarin manhajar Facebook ya karu da kashi 2.4 a cikin dari, a rahoton da jaridar Bloomberg ta rawaito.

DUBA WANNAN: Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ta kai ziyara Nijar

Mutum biyu da suka fi Zuckerberg a jerin sunayen sune wanda ya mallaki kamfanin nan na Amazon, Jeff Bezos da kuma shahararren attajirin nan wanda yake da kamfanin Microsoft, wato Bill Gates.

Jerin masu kudin duniya da Bloomberg keyi a kullum na Biloniyoyin duniya ya nuna hakan har a ranar Asabar dinnan data gabata.

Zuckerberg ya kai darajar dala biliyan 81.6, ya baiwa Buffet ratan kusan sama da dala miliyan 400, wanda yake shine shugaban kamfanin Berkshire Hathaway Investment group.

Kasuwancin Zuckerberg na California na filin sada zumunta kawai yana da sama da mutane biliyan 2 da ke amfani dashi duk wata.

Zuckerberg yayi alkawarin bada kashi 99 na jarin shi na Facebook a rayuwar shi, inji Bloomberg.

Zuckerberg ya fitar da dala biliyan 3.58 na hannun jarin shi na Facebook don wata kungiyar sadaka da ya hada da matar shi, Priscilla Chan a 2015.

Buffett ya bada kyautar hannun jari na kusan miliyan 290 a Berkshire Hathaway domin sadaka. daidai da kusan dala biliyan 50.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel