Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ta kai ziyara Nijar
Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Amina Muhammad ta kai ziyara Jamhuriyar Nijar, inda a jiya taje Jihar Maradi don gabatar da ziyarar gani da ido
Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Amina Muhammad ta kai ziyara Jamhuriyar Nijar, inda a jiya taje Jihar Maradi don gabatar da ziyarar gani da ido, akan irin ayyukan da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya ke yi a fannin ilimi, hakkokin yara, kiwon lafiya, da kuma kananan sana'o'i ga mata da kuma batun canjin yanayi a yankin.
DUBA WANNAN: 2019: Matasan Arewa sunce basu yadda shugaba Buhari ya zarce ba
A ranar Asabar din data gabata ne 7 ga watan Yulin wannan shekarar, Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ta kai ziyara Jamhuriyar ta Nijar din.
A bayanin da Amina Muhammad din ta yi, ta bayyana cewa babban makasudin ziyarar ta ta shine domin karfafa samar da hakkokin mata a fanin ilimi, lafiya da kuma karfafa musu guiwa wurin shiga harkar siyasa domin tafiyar da al'amuran mulkin kasashen yankin yanda ya kamata.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng