Aiki da cikawa: Sabon Shugaban kasar Malaysia ya damke tsohon Shugaba Rasak

Aiki da cikawa: Sabon Shugaban kasar Malaysia ya damke tsohon Shugaba Rasak

- An kama tsohon Shugaban kasar Malaysia Najib Rasak a hannu

- Ana zargin sa da laifin sace dukiyar kasar a lokacin yana mulki

- Za a gurfarnar da Rasak a gaban Kotun kasar ba da dadewa ba

Mun ji cewa Shugaban kasar Malaysia mai shekara kusan 93 Mohathir Mohammed ya sa an damke tsohon Shugaban kasar bisa zargin wawure dukiyar al’umma da yayi lokacin yana kan karagar mulki a kasar ta Malaysia.

Labarin da ke mu samu daga kasar waje sun ce an yi ram da tsohon Shugaban kasar Malaysia Najib Rasak da ya sauka ne kwanan nan bisa zargin da ke kan san a tafka mugun satar da ba a taba ganin irin sa a kasar ba.

KU KARANTA: An zabi 'Dan shekaru 93 yayi mulki a kasar Malaysia

Hukumar yaki da barayin Gwamnati na kasar za ta maka Rasak a gaban Kotu inda za a tuhume sa da laifin cin amanar kasa da kuma wuce gona da iri a Gwamnati. Idan an same sa da laifi dai za a daure sa na shekaru 20.

The Guardian ta rahoto cewa wata badakalar IMDB ce ta ci tsohon Shugaban don haka Hukumar da ke binciken barayin Gwamnati na kasar MACC ta kama tsohon Shugaban a gidan sa da ke Garin Kuala Lumpur kwanaki.

Ana dai zargin Shugaba Najib da satar dukiyar jama’a wanda ta kai Dala Miliyan 681 lokacin yana mulki don haka sabon Shugaban kasar ya nemi Jami’an kula da shiga-da-fice da su hana iyalin sa barin kasar tun da ya karbi mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng