Nigerian news All categories All tags
Sakon Iran ga Amurka: Mai zai kai dala dari ($100) kan kowacce garwa a kwanan nan

Sakon Iran ga Amurka: Mai zai kai dala dari ($100) kan kowacce garwa a kwanan nan

- Man da Iran ke fitar wa ga duniya ta hannun OPEC na sanya man yayi araha

- Idan Amurka ta sanya wa Iran takunkumi kar ta sayar da mai za'a sami gibi

- Wannan gibin zai sanya dole man ya haura dala 100 kan garwa daya a duniya

Sakon Iran ga Amurka: Mai zai kai dala dari ($100) kan kowacce garwa a kwanan nan

Sakon Iran ga Amurka: Mai zai kai dala dari ($100) kan kowacce garwa a kwanan nan

Saboda kokarin Amurka na ganin duniya ta ware kasar Iran, wadda ke kokarin lallai sai ta mulki duniyar musulmi ta hannun wani da suke jira wai shi Mahadi, Amurka na shirin kakabawa kasar takunkumi don kar ta sayar da mai a duniya.

Wannan kokari na Amurka, na zuwa ne bayan da ta fice daga yarjejeniyar da ta baiwa Iran din damar samun biliyoyin kudi saboda ta daina hada muggan makaman kare-dangi wanda take shirin yakar israila da Saudiyya dasu.

Shugaban Amurka Trump, aboki ga Larai da kasar Yahudu, yace kuskure ne a yarda da Mullolin Iran masu bakin rawani, wadanda ke dora shugaban kasa kuma sufadi yadda suke so kasar ta kasance, sabanin dimokuradiyya.

DUBA WANNAN: Zaki ya cinye mafarautan kananan dabbobi

Martanin Iran kan wadannan takunkumai dai, shine a wai ai man fetur, da iskar gas zasu yi wa duniiya tsada, inda take barazanar man na iya kaiwa dala 100 kan kowace ganga, abinda Turawa basu so.

Amurka dai, duk da iya tuggun ta,, na kokarin ganin an ware Iran ne har sai ta daina daukar nauyin ta'addanci a kasashen Musulmi, musamman kasar Labanon ta hannun Hizbolla.

Ita kuwa Iran, kokarita a kullum shine yada Shi'a da kakkabe Wahhabiyanci wanda tace shi ke kawo 'yan ta'adda irinsu Usama da Albaghdadi da Shekau.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel