Sojoji sun duba lafiyar yan farar hula a kyauta a garin Maiduguri (hotuna)
Domin karfafa dangantakar dake tsakanin sojoji da yan farar hula sannan kuma duk a shirye-shiryen raya ranar sojojin Najeriya, a ranar 3 ga watan Yuli soji sun gudanar da wani shiri na musamman a yankin Jiddari Polo Ground, Maiduguri.
Sojojin sun yi wa mutanen yakin gwaje-gwaje daban-daban tare da duba lafiyansu, sannan kuma suka basu magunguna da kulawa na musamman
Shugaban hafsan soji, Tukur Buratai ma ya ziyarci sojojin da suka samu rauni a asibiti domin tabbatar da cewa an basu kulawa na musamman sannan ya gode da irin aikin da suke yi tare da musu fatan samun lafiya.
Ga hotunan a kasa:
KU KARANTA KUMA: Muna maraba da dawowar yan sabuwar PDP - Lamido
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng