Tarihi zai bayar da mumunan labari akanmu idan aka cigaba da kashe-kashe - Dogara

Tarihi zai bayar da mumunan labari akanmu idan aka cigaba da kashe-kashe - Dogara

Kakakin majalisar wakilai, Mista Yakubu Dogara, ya bayyana cewa tarihi zai bayar da mumunan labari akan gwamnati mai mulki idan hart a gaza dakatar da yawan kashe-kashen bayin Allah da ake yi.

Dogara ya bayyana hakan a ranar Talata yayinda yake yiwa mambobin majalisar maraba da dawowa daga hutun karamar sallah.

Ya bayyana cewa ya zama dole a gaggauta dakatar da kashe-kashen bayin Allah da ake yi.

Tarihi zai bayar da mumunan labari akanmu idan aka cigaba da kashe-kashe - Dogara
Tarihi zai bayar da mumunan labari akanmu idan aka cigaba da kashe-kashe - Dogara

Kakakin majalisan ya bayyana cewa wannan lamari na kashe kashen bayin Allah ciki harda yara da mata da ake yi a fadin kasar abune da ya cancanci a koka.

KU KARANTA KUMA: Fayemi ya gana da Buhari a fadar shugaban kasa

Dogara ya kara da cewa lallai sai majalisar dokoki ta sake kokari don amfani da dukkanin ikon da kundin tsarin mulki ya bata da dama don ganin an tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin kasar ta hanyar taimakon hukumomin tsaro.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel