Buhari ya nemi ya ga Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya a gaban sa bayan Jami’an tsaro sun yi zanga-zanga a Borno
Mun samu labari cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikawa Sufeta na ‘Yan Sandan Najeriya Ibrahim K. Idris mni sammaci a makon nan saboda wata zanga-zanga da aka yi a Jihar Borno.
Fadar Shugaban kasa ta nemi Shugaban ‘Yan Sandan na Najeriya Ibrahim Idris ya bayyana a gaban ta bayan da wasu Jami’an ‘Yan Sanda su kayi zanga-zanga a Garin Maiduguri saboda rashin albashin su da wasu alawus.
Manema labarai sun bayyana mana cewa an hangi Sufeta Janar na ‘Yan Sanda Ibrahim Idris dazu a yau Litinin dinnan a hanyar ofishin Shugaban Ma’aikatan fadar Shugaban kasa watau Malam Abba Kyari a cikin Fadar Aso Villa.
KU KARANTA: An yi wani sauyi a gidan kwallon kafan Najeriya
Wata Majiyar ta ce ba shakka lambar Sufetan ‘Yan Sandan na Najeriya ya fito ne bayan da wasu Jami’an ‘Yan Sandan kasar su kayi zanga-zanga a babban birnin Jihar Borno inda su ka nemi a fito masu da wasu kudin su da su ka makale.
Rundunar ‘Yan Sandan Kasar dai ta karyata cewa Jami’an ta sun yi bore inda Mai magana da yawun Rundunar Jami’an tsaron Jimoh Moshood yace ‘Yan Sandan sun nemi a biya su kudin su ne kurum kafin su koma aiki kuma za ayi hakan.
Dazu kun ji cewa manyan Jam’iyyun adawan kasar nan sun gama shirye-shiryen yadda za su tika Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kasa a zabe mai zuwa na 2019.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng