Mayakan Boko Haram 32 sun mika wuya ga dakarun soji

Mayakan Boko Haram 32 sun mika wuya ga dakarun soji

Hukumar sojin Najeriya, ta bakin, texas Chukwu, darektan ta na hulda da jama’a, ta tabbatar da cewar mayakan kungiyar Boko Haram 32 sun saduda, sun mika wuya ga rundunar soji dake sassa daban-daban a Maiduguri.

Mayakan sun mika kansu da kansu ba tare da musayar wuta ko wata fafatawa ba, kamar yadda rundunar sojin ta sanar.

Daga cikin wadanda suka mika wuya akwai wani Mallam Ibrahim day a mika bindigarsa, samfurin AK47 dake dauke da alburushi 59, ga dakarun soji.

DUBA WANNAN: Shekau ba lafiya, yana cikin mawuyacin hali

Hukumar soji ta bayyana cewar, yanzu mayakan na amsa tambayoyi kafin daga bisani a mika su ga hukumomin da suka dace domin karasa tuhumarsu.

Mayakan Boko Haram 32 sun mika wuya ga dakarun soji
Mayakan Boko Haram 32 sun mika wuya ga dakarun soji

Mayakan Boko Haram 32 sun mika wuya ga dakarun soji
Mayakan Boko Haram da suka mika wuya ga dakarun soji

Mayakan Boko Haram 32 sun mika wuya ga dakarun soji
Mayakan Boko Haram 32 da mika wuya

A wani labarin Legit.ng, kun ji cewar, wani matashi, Saminu Ibrahim Magoli, dake zaune a unguwar Usubu ta karamar hukumar Kontagora a Jihar Neja na neman rasa hannunsa na hagu sakamakon dukan da jami'an 'yan sanda na ofishin shiyyar B a Kontagora suka yi masa.

Saminu, wanda ke sana'ar wankin mota, shine ke rike da ragamar gidansu kasancewar iyayensa marasa karfi ne, kamar yadda Rariya suka rawaito.

Da yake shaidawa Rariya yadda lamarin ya faru, Saminu ya ce, "Ina wurin sana'a ta, wankin mota, ranar Sallah sai ga wasu mutane sun zo suna tambayar wani abokin aikina, Muhammad Tauhid M.T, sai nace masu bani da masaniyar inda yake domin yakai kimanin kwanaki 5 bai fito wurin aiki ba, daga fadin haka sai kawai suka kama ni suna kokarin jefani a motar su, na ce masu ni ba zan je ko ina ba tunda banyi laifin komai ba wanda kuma suke nema bansan laifin da yayi ba.

Sannan ya cigaba da cewar "Da zuwanmu suka saka ni a Sel suka kulle, can saiga wani dan sanda ya zo da gora ya hau duka na har ya karya mani kafada, duka na kawai yake yi ko ta ina gashi ina fama da ciwon yatsa (Karkare). Duk jikina sida ya kumbura amma duk da hakan nan suka barni har gari ya waye.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel