Tsawon shekaru 2 kenan da mijina ya kaurace mani don haka ba zan iya cigaba da zama da shi ba – Wata mata ga kotu

Tsawon shekaru 2 kenan da mijina ya kaurace mani don haka ba zan iya cigaba da zama da shi ba – Wata mata ga kotu

Rahotanni sun kawo cewa wata mata da aka ambata da suna Monsurat Ogundipe ta yi karar mijinta a wani kotu dake Agege, jihar Lagas inda ta nemi a raba auransu.

A cewar Mansurat tsawon shekaru biyu kenan da mai gidan nata da aka ambata da suna Sheriff ya kaurace mata.

Mansurat ta shaida wa kotu cewa bayan kin kulata da ya ke yi, ya kuma kasance tataccen mashayin giya, domin kullum a buge ya ke dawowa gida.

“Gaba daya yanzu hankalin Sheriff mijina baya muradi na da’ya’ya na. Shi dai ya sha giyar sa ya kuma nemi matan banza a waje ne ya sa a gaba.

Tsawon shekaru 2 kenan da mijina ya kaurace mani don haka ba zan iya cigaba da zama da shi ba – Wata mata ga kotu
Tsawon shekaru 2 kenan da mijina ya kaurace mani don haka ba zan iya cigaba da zama da shi ba – Wata mata ga kotu

Shi ko mijin Mansurat Sheriff bai musanta wannan korafin da Mansurat ta yi a kan sa ba sai dai ya ce yayi haka ne domin ya dawo wa kansa daraja da kima a matsayin sa na mijinta. Yace Mansurat ta raini sannan bata ganin shi da gashi ko kadan.

KU KARANTA KUMA: Wani kyakyawan matashi ya auri mata biyu a rana daya ya karfafawa sauran maza gwiwar yin haka

A karshe alkalin kotun Ibironke Elabor ya shawarce su da su koma gida su sassanta kan su. Sannan ya daga shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Yuli.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa ko Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng