Inna Lillahi wa Inna Ilaihi rajiun: Kananan Yara 500 sun mutu a Zamfara
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa akalla kananan yara guda dari biyar ne suka rasa rayukansu a jihar Zamfara sakamakon gubar karfe, kamar yadda gwamnan jihar, Abdul Aziz Yari ya bayyana, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.
Yari ya bayyana haka ne a yayin wani taron kara ma juna sani akan hadduran dake tattare da hakar gwal a Najeriya da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja, inda yace adadin kananan yara da suka rasu a sakamakon gubar karfe a shekarar 2010 sun kai dari biyar, ba dari hudu ba, kamar yadda wasu ke fadi ba.
KU KARANTA: Tsokalo tsuliyar Dodo: Yan bindiga sun hallaka Dakarun Sojoji guda 2
Legit.ng ta ruwaito Yari ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Farfesa Abdullai Shikafe, inda yace yawancin yaran da mutuwar ta shafa yan kasa da shekara biyar ne, yayin da wadanda suka sha kuwa suna fama da matsalar tunani.
Wannan guba dai ana samunsa ne a cikin kasa, musamman a yayin da ake aikin tsaftace ma’adanan kasa da nufin gano zinari a cikinsa, kuma ya kan harbi sassan jikin dan Adam, musamman kananan yara, inda yake taruwa a hakora da kasusuwan mutum.
Sai dai gwamnan yace duk wannan ya faru ne kwanaki goma y agama mulki, amma da hawansa ya tattaro kwararrun likitoci da jami’an kiwon lafiya tare da hadin gwiwa da gwamnatin tarayya, inda aka samu nasarar dakile cutar.
Jihohin da wannan lamar ya fi shafa sune jihar Neja, Zamfara da Kebbi, inda ko a shekarar 2016 sai da cutar ta kashe mutame 28 a jihar Neja, yayin da jihar Zamfara ta kashe naira miliyan 150 wajen maganceta.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng