Wani babban basarke a Zamfara ya bayyana silar kashe-kashen mutane a jihar

Wani babban basarke a Zamfara ya bayyana silar kashe-kashen mutane a jihar

Sarkin Tsafe wanda akafi sani da Yandoton Tsafe, Alhaji Muhammadu Bawa ya ce shaye-shayen miyagun kwayoyi ne umml aba'isin fitintinun da ke faruwa a Jihar.

A yayin da ya ke karbar bakuncin wata tawagan hukumar yaki da miyagun kwayoyi na kasa NDLEA a fadar sa, Sarkin wanda ya samu wakilcin daya daga cikin hakiminsa, Sarkin Gabas Alhaji Aliyu Abubakar Aliyu ya koka kan yadda matasa ke shan miyagun kwayoyi.

Wani babban basarke a Zamfara ya bayyana silar kashe-kashen mutane a jihar
Wani babban basarke a Zamfara ya bayyana silar kashe-kashen mutane a jihar

"Mafi yawancin 'yan barandan suna aikata barnarsu ne bayan sunyi tatil da miyagun kwayoyi kuma hankulansu ta gushe kuma masarautar a shirye ta ke don yin gwiwa da masu ruwa da tsaki don magance matsalar," inji shi.

KU KARANTA: Zan kawo karshen kashe-kashe idan aka zabe ni shugaban kasa - Makarfi

Jami'an NDLEA sun kai ziyara fadan sarkin ne a karkashin jagorancin kwamandansu Mr. Adamu Gabriel Eigege don murnar zagayowar ranar yaki da ta'amulli da miyagun kwayoyi na majalisar dinkin duniya.

A jawabinsa, ciyaman din karamar hukumar Tsafe, Alhaji Aliyu MC ya ce gwamnatinsa a shirye ta ke don taimakawa wadanda ke son barin shaye-shaye a karamar hukumar.

Ya kuma ce a matsayinsa na dan siyasa, ba zai taba zuwa karbo belin duk wani wanda aka kama yana ta'amulli da miyagun kwayoyi ba ko da dan cikin sa ne.

Ya kuma shawarci matasa su kasance masu biyaya ga doka da oda kuma su guji shaye-shayen miyagun kwayoyi saboda su kasance masu kawo cigaba a unguwaninsu da garuruwansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel