Zaben 1993: Yadda ta kaya tsakanin Abiola da Uwar mu a kan Janar Babangida – Kola Abiola
Kola Abiola wanda shi ne babban ‘Dan Marigayi Mashood Kashimawo Abiola ya bayyana yadda ta kasance tsakanin Mahaifiyar sa da Mahaifin su wanda kusan ya lashe zabe amma aka hana mulki.
Mun samu labari daga bakin Kola Abiola cewa Mahaifiyar sa Simbiat Atinuke Abiola wanda mai dakin Marigayin ‘Dan siyasar ne ba ta so Abiola ya nemi takarar Shugaban Kasa lokacin Janar Ibrahim Babangida yana mulki ba.
Babban ‘Dan MKO Abiola ne ya bayyana wannan da kan sa kwanan nan inda yace Mahaifiyar ta sa Simbiat Abiola ta ba MKO Abiola shawara ya hakura da neman mulki muddin Janar IBB yana rike da kasar a lokacin mulkin Soji.
KU KARANTA: Ana zargin wata babban Lauya da kashe mijin ta da kan ta
Mista Kola Abiola ya bayyana wannan ne lokacin da ya fito a wani shirin siyasa da aka shirya a Gidan Talabijin na TVC. Abiola yace maganar da ake yadawa na cewa Simbiat Abiola ta amince Mijin ta ya tsaya takara a 1993 karya ne.
‘Dan Marigayin yace Mahaifiyar ta su ba ta so Abiola yayi takara a zaben 1993 ba, ana ta shawarar ta so ne ya bari sai bayan Babangida ya bar mulki. Ko da Abiola dai ya saye fam din takarar yayi kokarin boyewa iyalin na sa amma a banza.
Ku na da labari cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari dai ya karrama MKO Abiola da kuma Babagana Kingibe da lambar girma saboda abin da ya faru a zaben 1993. Iyalan Marigayin sun ji dadin wannan abu da Gwamnatin Taraya tayi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng