Tsohuwar minista ta amayar da miliyoyin kudin makamai da ta hadiya bayan ta ji matsar EFCC

Tsohuwar minista ta amayar da miliyoyin kudin makamai da ta hadiya bayan ta ji matsar EFCC

- Hukumar EFCC mai yaki da cin da rashawa ta shiadawa wata kotun gwamnatin tarayya dake zaman ta Legas cewar, tsohuwar minister Abuja, Jumoke Akinjide, ta dawo da miliyan N650m

- Ana Akinjide da karbar kudin ne gabanin zaben shekarar 2015

- Jami’in hukumar EFCC, Usman Zakari, ya bayyana cewar sun karbi kudin daga hannun Akinjide

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta bayyana cewar tsohuwar minister Abuja, Jumoke Akinjide, ta dawo da kudi, miliyan N650 da ta karba gabanin zaben shekarar 2015.

Tsohuwar minista ta amayar da miliyoyin kudin makamai da ta hadiya bayan ta ji matsar EFCC

Olajumoke Akindije

Jaridar The Nation ta rawaito cewar an gurfanar da Akinjide tare da wani jigo a jam’iyyar PDP a jihar Oyo, Cif Olarenwaju Otiti, sanatan jihar Oyo ta tsakiya da kuma tsohuwar minister amn fetur, Diezani Madueke, da yanzu bat a Najeriya.

DUBA WANNAN: Babu wanda zai iya daure ni saboda na kiyaye mutunci na – Shugaba buhari ya cikawa ‘yan adawa baki

Jam’in hukumar EFCC, Usman Zakari, ya tabbatar wad a kotu batun dawo da kudin tare da bayyana ceawr, da farko mijin ta ne ya fara biyan miliyan N10 daga cikin kudin klafin daga bisani wasu jam’ian na EFCC karkashin jagorancin Shu’aibu Shehu, su karbo ragowar miliyan N640 daga hannun ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel