Ko wa zai zama Mataimakin Gwamnan Jihar Kano daga 2019 – 2023?

Ko wa zai zama Mataimakin Gwamnan Jihar Kano daga 2019 – 2023?

Labari ya zo mana daga Jaridar Daily Trust cewa yanzu haka a Jihar Kano an fara lissafin wanda zai zama Mataimakin Gwamnan Jihar Kano bayan zaben 2019 ganin cewa an samu matsala tsakanin Mataimakin Gwamna da Mai gidan sa.

Ko wa zai zama Mataimakin Gwamnan Jihar Kano daga 2019 – 2023?

Hafiz Abubakar ya nuna cewa ba zai tafi da Ganduje ba

Bisa dukkan alamu dai Farfesa Hafiz Abubakar ba zai cigaba da tafiya da Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ba. Daga cikin wandada ake tunani za su maye gurbin sa akwai Abdullahu Abbas, Babba Dan Agundi, Alhassan Doguwa da wasun su.

Ga dai manyan ‘Yan siyasan da ake tunani cikin za a samu wanda zai tafi da Ganduje idan ya zarce a 2019:

1. Abdullahi Abbas

Abdullahi Abbas wanda shi ne Shugaban Jam’iyyar APC a Kano na iya maye gurbin Hafiz Abubakar ganin girman gidan da ta fito da kuma cewa Yankin sa daya da Mataimakin Gwamna mai-ci.

2. Muhammad Garba

Kwamishinan yada labaran Jihar yana cikin wadanda ke gaba-gaba a Gwamnatin Ganduje kuma tun-ba-yau-ba su ke tare. Ana tunani yana cikin wadanda Ganduje zai iya zaba su yi masa Mataimaki a 2019.

3. Munir Dan Agundi

Honarabul Babba Dan Agundi yana cikin mutum 6 da ake tunani Gwamna zai iya zaba a matsayin Mataimakin sa bayan zaben 2019. Dan Agundi yana cikin manyan ‘Yan Majalisar Tarayya daga Kano kuma yana da magoya.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Jam’iyyar APC ta canza salon taken ta wajen taron ta na kasa

4. Abdullahi Yusuf Ata

Ata wanda wanda shi ne Kakakin Majalisar dokokin Jihar Kano yana tare da Gwamna Ganduje. Masu harsashe sun ce Ganduje na iya dauko Ata a matsayin Mataimakin sa domin kawo karshen rikicin Majalisar Jihar.

5. Alhassan Doguwa

Hon. Ado Doguwa yana cikin ‘Yan gaban goshin Gwamna Ganduje kuma rikakken ‘Dan siyasa ne wanda yake da Mabiya. Masu harsashen lamarin siyasa sun ce ana iya tafiya da babban ‘Dan Majalisar a 2019.

6. Nasiru Gawuna

Wasu a na su hangen su na kawo cewa Mai Girma Gwamna Ganduje zai iya daukar Kwamishinan sa Nasiru Gawuna ya maye gurbin Farfesa Hafiza Abubakar wanda shi har yanzu yake rike da jar hular sa kamar a da.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel