Yanzu-yanzu: Jam’iyyar APC ta tashi daga ‘canji’ zuwa ‘cigaba’ – APC
- Dazu aka sauya salon taken APC a wajen taron Jam'iyyar mai mulki
- A wajen babban gangamin APC na kasa aka sakewa Jam'iyyar take
- Ana kokarin maida taken Jam'iyyar APC cigaba a maimakon canji
Mun samu labari cewa yayin da ake gangamin Jam’iyyar APC mai mulki a Birnin Tarayya Abuja. Jam’iyyar ta kawo wani sabon salo inda ta canza taken ta daga ‘canji’ kamar yadda aka san ta da shi.
Labarin nan ya zo mana dazu nan ne daga Jaridar Vanguard ta kasar nan cewa a wajen gangamin Jam’iyyar wani daga cikin masu jawabi ya sanar da cewa ya kamata a sauya taken Jam’iyyar mai mulki daga canji zuwa cigaba.
KU KARANTA: Sababbin Shugabannin Jam'iyyar APC da aka zaba
Sai dai kuma kafin a iya canzawa Jam’iyyar take sai an sakewa kundin tsarin Jam’iyyar garambawul. Layi na 4 na tsarin dokokin Jam’iyyar ya bada dama ake yi wa take da ‘canji’ ma'ana watau za a kawo sauyi wajen mulki a kasar.
Kafin nan dama Jam’iyyar PDP ta kawo wani sabon salo inda ta ke cewa ‘a canza canji’. PDP ta kawo wannan take ne domin ganin ‘Yan kasar sun yi watsi da Jam'iyyar APC a zaben 2019. A 2015 ne APC ta ba PDP kashi ta karbe mulki.
Jiya kun ji labari cewa Kwamared Adams Oshiomhole ne ya zama sabon shugaban Jam’iyyar APC mai mulki. Tsohon Gwamnan Edo ya godewa goyon-bayan da ya samu daga ‘Ya ‘yan Jam’iyyar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng