Bayan sun gama soye wa ta sulale cikin dare da katinsa na banki, leka kuji nawa ta caje shi

Bayan sun gama soye wa ta sulale cikin dare da katinsa na banki, leka kuji nawa ta caje shi

Wani dan kasuwa ya dibo ruwan dafa kansa yayin da budurwarsa ta sace masa katin ATM kuma ta cire zunzurutun kudi N1 miliyan daga asusun ajiyar bankinsa kuma ta kama gabanta.

An gano cewa matar mai suna Thelma Kiberly wanda ke zaune a Fatakwal a jihar Rivers ta ziyarci sahibin nata ne mai suna Olugbenga a gidansa da ke Victoria Islanda a Legas a ranar 17 ga watan Mayun 2018.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa masoyar sun kewaya wuraren shakatawa a cikin gari kafin suka komo gida don cigaba da more soyayarsu.

Bayan barci ya kwashe Olugbenga mai shekaru 45 bayan sun gama cinye soyayarsu a gado sai Kimberly mai shekaru 22 da dauke katin ATM dinsa da wayar salulan sa.

DUBA WANNAN: Lafiya jari: Illoli 5 da shan ruwan sanyi keyi a jikin dan-adam

An ce ta yi cire kudi kuma tayi amfani da katin ATM din wajen yin sayaya a wata katafaren shago a Lekki ta hanyar amfani da PoS.

Olugbenga ya shigar da kara ofishin yan sanda da ke Ikoyi kuma a hankali an gano inda Kimberly ta ke a cikin wannan watan.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa yayin da Kimberly ke buya don kada yan sanda su kama ta, an umurci bankinta su sanya takunkumi a kan asusun ajiyarta.

Daga nan kuma sai Olugbenga ya aike da N100,000 zuwa asusun bankinta don kafa mata tarko, ganin alert ke da wuya sai Kimberly ta garzaya banki don cire kudin kuma a nan ne yan sanda suka damke ta.

Bayan an kama ta, Kimberly ta shaida wa yan sanda cewa ta hadu da Olugbenga ne a shekarar 2016 a Fatakwal lokacin da ya ziyarci mai rikon ta wanda abokinsa ne. Ta cigaba da cewa a ranar 17 ga watan Mayu ta ziyarci shi a gidansa a Victoria Island inda suka fita sayaya kuma daga baya suka koma gida suka kwanta tare.

"Daga nan ne na dauke ATM dinsa bayan ya yi barci kuma na cire N150,000 a Obalande da Victoria Island da Ikeja. Na kuma tafi shago a Lekki inda na kashe N363,000, na biya ta PoS" inji ta.

Kakakin yan sanda na jihar Legas CSP Chike Oti ya ce za'a a gurfanar da ita a gaban wata kotun Majisatare da ke Tinubu don yi mata shari'a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel