Buhari ya dawo da wasu manyan ma'aikatan gwamnati da aka dakatar tun 2015

Buhari ya dawo da wasu manyan ma'aikatan gwamnati da aka dakatar tun 2015

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin a mayar da wasu manyan sakatorin hukumomin gwamnati uku da aka dakatar tun shekarar 2015.

Direktan labarai na ofishin sakataren gwamnati, Lawrence Ojabo ne ya bayar da sanarwan a jiya Juma'a a garin Abuja.

Kamar yadda Mr Ojabo ya bayyana, manyan sakatarorin sune Ibukun Odusote da Nkechi Ejele da kuma Fatima Bamidele.

Buhari ya dawo da wasu manyan ma'aikatan gwamnati da aka dakatar tun 2015
Buhari ya dawo da wasu manyan ma'aikatan gwamnati da aka dakatar tun 2015

DUBA WANNAN: Lafiya jari: Illoli 5 da shan ruwan sanyi keyi a jikin dan-adam

Kamfanin dillanci labarai NAN ta ruwaito cewa Ms Bamidele na aiki ne Ma'aikatar Neja-Delta yayinda Ejele na aiki ne da Ma'aikatan Al'adu da wayar da kan kasa kana Odusote na aiki ne da Ma'aikatar Noma da raya karkara.

An dai dakatar da ma'aikatan gwamnatin ne a Nuwaban shekarar 2015 bisa zarginsu da aikata wasu laifuka.

Sai dai a cikin kwanakin nan ne Ms Bamidele tayi murabus daga aiki bayan da cika shekaru 60 da haihuwa a duniya kamar yadda dokar aikin gwamnati ya tanada.

Mr Ojabo ya ce shugaban kasar ya bayar da umurnin ne lokacin da ya ke bita a kan rahoton da Kwamitin ayyukan gwamnatin tarayya da ofishin sakataren gwamnatin tarayya suka bashi.

Shugaban kasan ya bayar da umurnin mayar da su bakin aikinsu ne saboda ba'a samu gamsasun hujja na cewa sun karya dokokin aiki ba bayan gudanar da binciken.

"Mayar da su bakin aikin su da akayi ya nuna cewa gwamnatin tarayya na bin didigi wajen ganin cewa ba'a musgunawa wani ma'aikaci saboda zargi mara tushe," inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel