Yan sanda sun kama ýan Shi’a 9 a Kaduna
A ranar Juma’a, 22 ga watan Yuni, rundunar yan sandan Kaduna ta sanar da kamun yan kungiyar Shi’a tara akan harin da aka kaiwa jami’an yan sanda a jihar.
Kwamishinan yan sandan jihar, Mista Austin Iwar, ya bayyana hakan a wata sanarwa da sa hannun kakakin yan sandan Mista Muktar Aliyu a Kaduna.
Aliyu ya tabbatar da kashewani jami’’in dan sanda a lokacin harin.
Yace hukumar ta zuba jami’ai daga sashin kwararru domin gano shugabanni da wadanda suka jagoracin kai harin.
KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin sama ta kaddamar da gaggarumin aiki ga jami’anta dake Abuja (hotuna)
Ya bayyana yunkurin a matsayin kokarin tursasa yan sanda rikici da kungiyar domin ta da zaune tsaye a jihar.
A ranar Alhamis ne rikici ya kaure tsakanin jami'an yan sanda da yan kungiyar Shi'a akan cigaba da tsare shugabansu Ibrahim El-Zakzaky.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng