Dakarun SARS sun cika hannu da wasu masu garkuwa da mutane dake amfani da kayan Yansanda
Jami’ain rundunar Yansanda dake yaki da fashi da makami, SARS sun samu nasarar kama wasu gungun matasa da suka yi kaurin suna wajen amfani da kayan Yansanda da Motar Yansanda wajen yin garkuwa da mutane tare da musu fashi a jihar Ribas.
Legit.ng ta ruwaito yan fashin suna amfani da wata Mota kirar Ford Jeep, wanda suka yi mata Fenti, sak irin fentin motocin Yansandan Najeriya, sa’annan suka nemi sulke irin irin na Yansanda suka rubuta ‘Police’ a jikinsa.
KU KARANTA: Babban labari: Abubuwa guda 3 da suka taba sanya Buhari fashewa da kuka
Rundunar Yansandan jihar Ribas tace ta sama nasarar kama yan fashin ne a ranar Talata, 19 ga watan Yuni, inda tace ta kama bindigu guda biyu kirar ‘Pump Action’, sa’annan ya bayyana sunayensu kamar haka:
Tony Rapheal
Ifanyi Okoye
Chigozie Onuigbo
Emeka Nwaiwu
Clark Sunday.
Chinedu Isia
Barayin sun tabbatar ma Yansanda cewa sau dayawa mutane su kan saki jiki dasu akan Yansanda ne su, ta haka ne suke tafiya dasu don yi garkuwa dasu har sai an biya kudin fansa, idan kuma ba’a biya ba su kashe mutum.
Daga karshe sanarwar ta bayyana hukumar Yansanda za ta cigaba da budanar da binciken kwakwaf kan yan fashin, daga bisani kuma ta mika su gaban Kotu don fuskantar hukunci, da zarar ta kammala bincike.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng