12 ga watan Yuni: Dubi yadda Buhari ya karrama Moshood Abiola

12 ga watan Yuni: Dubi yadda Buhari ya karrama Moshood Abiola

A yau Laraba, 12 ga watan Yuni, Shugaban kasa Muhammadu Buhar ya karrama marigayi Moshood Abiola da babbar lambar yabon kasar a babban birnin tarayya domin tunawa da zaben 12 ga watan Yunin 1993.

Shugaban kasa Buhari ya mika duk wasu takardu da suka kamata don karramawar ga iyalan marigayi Abiola.

12 ga watan Yuni: Dubi yadda Buhari ya karrama Moshood Abiola
12 ga watan Yuni: Dubi yadda Buhari ya karrama Moshood Abiola

KU KARANTA KUMA: Kasar Ghana, da sauran kasashen Afrika zasu dunga siyan mai daga matatar Dangote

Dan marigayin Kola shi ne ya karbi lambar yabon ta GCFR a madadin mahaifinsa yayin taron, wanda aka gudanar a fadar Aso rock.

Ga hotunan taron a kasa:

12 ga watan Yuni: Dubi yadda Buhari ya karrama Moshood Abiola
12 ga watan Yuni: Dubi yadda Buhari ya karrama Moshood Abiola

12 ga watan Yuni: Dubi yadda Buhari ya karrama Moshood Abiola
12 ga watan Yuni: Dubi yadda Buhari ya karrama Moshood Abiola

12 ga watan Yuni: Dubi yadda Buhari ya karrama Moshood Abiola
12 ga watan Yuni: Dubi yadda Buhari ya karrama Moshood Abiola

A halin da ake ciki, wani dan takarar gwamna a karkashin inuwar All Progressives Congress (APC) a zaben jihar Osun da zaa yi a ranr 22 ga watan Satumba, Alhaji Moshood Olalekan Adeoti ya shawarci tsohon shugaban kasa a mulkin soja, janar Ibrahim Babangida da ya ba yan Najeriya hakuri akan juyin mulkin 12 ga watan Yunin 1993.

Adeoti wanda ya kasance sakataren gwamnatin jihar Osun ya yabama shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kaddamar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar Damokradiyya da yayi tare kuma da karrama marigayi Moshood Abiola.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel