Dandalin Kannywood: Shawara ta ga mata wadanda ke son shigowa fim - Fatima Abubakar Shu'uma

Dandalin Kannywood: Shawara ta ga mata wadanda ke son shigowa fim - Fatima Abubakar Shu'uma

Shararriyar jarumar nan ta wasan fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood ta baiwa dukkan masu sha'awar shiga a dama da su a harkar fina-finai musamman ma mata da su tabbata sun samu amincewar iyayen su tukuna.

Jarumar dai ta bayyana hakan ne a lokacin da ake fira da ita a gidan talabijin din nan na Hausa na Arewa24 a cikin shirin Ga Fili Ga Mai Doki na Kundin Kannywood tare mashiryin shirin Jarumi Aminu Shariff.

Dandalin Kannywood: Shawara ta ga mata wadanda ke son shigowa fim - Fatima Abubakar Shu'uma
Dandalin Kannywood: Shawara ta ga mata wadanda ke son shigowa fim - Fatima Abubakar Shu'uma

KU KARANTA: Ganawar Saraki da jaruman Kannywood ta bar baya da kura

Legit.ng ta samu cewa duk dai a cikin firar, jarumar ta kuma shawarci matan da su zama masu hakuri musamman ma da masoyan su da a kullum za su yi ta yin tururuwa domin kawowa gare su.

Haka ma dai jarumar ta bayyana cewa jaruma Jamila Nagudu ce tafi burge ta a cikin jaumai mata sannan kuma Adam A. Zango ne yafi burge ta a cikin jarumai maza a masana'antar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel