Yariman Saudiyya ya bai wa yar fim din Amurka Kristen dala 500k don hirar mintina 15
Wani mutumin kasar Amurka mai suna Harvey Winston, wanda ya kasance tsohon dogari a kasar Saudiyya ya bayyana cewa daya daga cikin yarimomin masarautar Saudiyya ya baiwa fitaciyyar jarumar fim din Amurka, Kristen Stewart kudi har dala dubu dari biyar ($500,000).
Ya bata kudin ne saboda kawai su debewa juna kewar mintuna 15 ta hanyar hira.
A cewar Winston, Stewart ta amsa fayyatar da yariman yayi ma ta, sannan ta bukaci a zuba kudaden a asusun wata gidauniya mai rajin taimakawa wadanda ibtila’in ambaliyar ruwa ta cika da su a kasar Ostireliya.
KU KARANTA KUMA: Abunda na fadama su Ali Jita da sauran matasa da suka kawo mun ziyara – Shugaba Buhari
An sanar da cewa yariman wanda ba a bayyana sunansa ba,yana matukar kaunar 'yar fim din.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng