'Daukan Aiki: Hukumar 'Yan sanda ta saki Jerin Sunayen Mutanen da suka yi Nasara

'Daukan Aiki: Hukumar 'Yan sanda ta saki Jerin Sunayen Mutanen da suka yi Nasara

Da sanadin shafin Jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, hukumar 'yan sanda ta Najeriya ta saki jerin sunayen wadanda suka taki nasara wajen daukar su aiki na hukumar a shekarar 2018 bayan ta gudanar da tantancewa a matakai daban-daban.

A ranar yau ta Juma'a hukumar ta wallafa jerin sunayen mutane da suka taki nasara ta samun damar daukar su wannan aiki na jami'an tsaro.

'Daukan Aiki: Hukumar 'Yan sanda ta saki Jerin Sunayen Mutanen da suka yi Nasara
'Daukan Aiki: Hukumar 'Yan sanda ta saki Jerin Sunayen Mutanen da suka yi Nasara

Hukumar da sanadin wani babban ma'aikacin ta, Abayomi Shogunle, da ya bayyana a shafin sa na dandalin sada zumuntar tuwita, ya bayyana jerin sunayen Mutanen da suka yi nasara ta daukar su aiki.

KARANTA KUMA: Gwamnati ta rarraba Kayan Agaji ga Nakasassu da Talakawa a jihar Kebbi

Babban Jami'i Abayomi ya nemi al'ummar Kasar nan da suke nemi shiga aikin na 'yan sanda akan su duba sunayen su da ranar da za a fara horas da su a shafin hukumar kamar haka; https://psc.org.ng/candidateslist/

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar ta kayyade ranar 08/06/2018 a matsayin ranar fara karbar horo, inda ta bayar da talala har zuwa ranar 13/06/2018. Ta kuma yi gargadin duk wanda ya wuce wannan rana to ya yi asarar aikin sa.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan daukar aiki na hukumar 'yan sanda ya biyo bayan umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na daukar sabbin jami'ai 6, 000 a fadin Kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel