Kuyi hattara da masu bude shafukan bogi da sunana – Hadiza Gabon

Kuyi hattara da masu bude shafukan bogi da sunana – Hadiza Gabon

Fitaciyyar jarumar nan ta kamfanin shirya fina-fina hausa na Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon ta ja hankalin mabiya shafinta na zumunta kna su hankalta da masu bude shafuka na bogi da sunanta.

Jarumar ta wallafa wani shafi na bogi da aka bude da sunan ta wanda ke rokon jama'a da su tallafa da kudi domin tallafawa marasa karfi.

Ta nisantar da kanta daga shafin tare da yin kira ga jama'a da su kauracewa ire-iren shafukan bogi masu bukatar kudi daga masu bibiyan ta.

wannan yana daya daga cikin abubuwa dake ci ma jaruman kannywood tuwa yadda ake yawan bude shafukan bogi da sunan su tare da neman kudi daga jama'a.

Kuyi hattara da masu bude shafukan bogi da sunana – Hadiza Gabon
Kuyi hattara da masu bude shafukan bogi da sunana – Hadiza Gabon

A baya Legit.ng ta kawo maku hotunan yadda jarumar tayi rabon kayayyakin abinci na azumi da kayan sallah ga marasa karfi a farkon watan Ramadana.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta ba Dino Melaye hutu don ya tafi kasar waje yin magani

Babu mamaki wannan halin alkhairi na jarumar ne ya janyo hankulan mutane har suke son yin amfani da damar wajen yaudarar mutane da sunanta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Domin samun ingantattun labarai ku bide mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel