Matakan tsige shugaban kasa 8 a kundin tsarin mulkin Najeriya

Matakan tsige shugaban kasa 8 a kundin tsarin mulkin Najeriya

Ana ci gaba da yamutsa gashin baki kan barazanar da majalisar dokokin kasar tayi na tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A ranar Talata, 5 ga watan Yuni ne majalisar tayi barazanar tsige Buhari idan har bai kiyaye wasu sharuda da ta gindaya masa ba.

Hakan ya dan haifar da rabuwar kai inda wasu ke goyon bayan shugaban kasar.

Don haka muka yi amfani da wannan dama wajen kawo maku wasu matakai da kundin tsarin mulkin kasar Najeriya ta gindaya wajen tsige shugaban kasa.

Matakan tsige shugaban kasa 8 a kundin tsarin mulkin Najeriya
Matakan tsige shugaban kasa 8 a kundin tsarin mulkin Najeriya

Gasu kamar haka:

1. Karon farko sai an samu akalla kashi 1 cikin 3 na Sanatoci da mambobin Majalisar wakilai kowanen su ya sa hannu a kan jerin laifukan da suke tukumar Shugaban Kasa da su. Sannan sai su aikewa Shugaban Majalisar Dattawa wasikar bukatar su ta neman tsige shugaban tare da kwafen takardar da ke dauke da laifukan da ya aikta.

Laifin shugaba: Kamar yadda dokar Najeriya ta gindaya, “ya kasance Shugaban Kasa ya karya wasu dokoki na Najeriya a wajen tafiyar da mulkin sa, ko kuma wani abu na ba daidai ba wanda majalisar ta gamsu da cewa ya aikata ba daidai ba.

2. Dole ya kasance cikin kwanaki bakwai Shugaban Majalisar Dattawa ya aikewa Shugaban Kasa da kowane Dan Majalisa da Sanata kwafen wasikar, wacce ke dauke da zarge-zargen tuhumar da ake yi masa.

3. Shugaban Kasa na da damar maida musu da amsa, ko kuma ba sai ya maida musu da amsa ba, duk daya. Amma idan har zai maida amsa, to ya kasance tilas wasikar ta isa ga dukkan Sanatoci da ‘yan Majalisar tarayya.

4. A cikin kwanaki 14 da karbar takardar neman tsige Shugaban Kasa, zai kasance Majalisar Tarayya da Majalisar Dattawa sun yi zama a majalisar su domin su amince da cewa shin akwai bukatar a binciki zargin ko kuwa? Sai akalla kashi 2 bisa 3 na mambobin sun amince tukunna.

5. Idan har yunkurin ya kasa samar da adadin yawan ‘yan majalisar da za su goyi bayan sa, to sai nan da nan a dakatar da yunkurin tsigewar. Ba za a sake daukar wani mataki ba. Amma idan an samu yawan adadin da akalla ake bukata na masu son a tsige shugaban ya kai yadda doka ta gindaya, to a cikin kwana bakwai da amincewa sai Shugaban Majalisar Dattawa ya umarci Babban Cif Joji na Tarayya ya kafa kwamiti na mutane 7, wadanda ya ke ganin cewa mutane ne masu gaskiya, amana kuma wadanda ake kyautata wa adalci domin su bincki zarge-zargen da Majalisa ta yi wa Shugaban Kasa.

Sannan kuma ya kasance daga cikin mambobin babu ma’aikacin gwamnati kuma babu dan majalisar dattawa ko ta tarayya.

6. Ya kasance kwamitin bincike ya bayar da sakamakon binciken da ya yi a cikin watanni uku. Za su bada sakamakon binciken ga Majalisar Dattawa da ta Tarayya.

A lokacin da kwamitin ke binciken sa, Shugaban Kasa na da damar kare kan sa, kuma ya na da damar da zai tura lauyan sa ya kare shi a madadin sa.

KU KARANTA KUMA: Tsige Buhari za mu yi tunda dai shi ba Allah bane – Jagaba

7. Idan kwamitin bincike ya bada rahoton cewa ba a kama Shugaban Kasa da tafka laifi ba, to ba za a kara daukar wani mataki ba. Amma idan kwamitin bincke ya kama Shugaban Kasa da laifi, sai Majalisa su amince da rahoton, sannan su dauki haramar zartas da kudirin tsige shi.

8. Sai kashi 2 bisa 3 na Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya sun amince a tsige shugaban kasa sannan za a ce ya tsigu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Domin samun ingantattun labaranmu bide mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel