An gano rishon Biliyan 9 da Jonathan ya saya bayan shekaru 3

An gano rishon Biliyan 9 da Jonathan ya saya bayan shekaru 3

A 2015 ne Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya bayyana cewa Gwamnatin sa za ta kashe Naira Biliyan 9 wajen sayan rishon zamani domin girki. Har yanzu wannan risho da Jonathan ya bada kwangila su na nan a ajiye a Abuja a banza.

A wancan lokacin Gwamnati ta ware kudi har tsaba Biliyan 9 domin a rabawa Mata kusan 90, 000 rishon da ba ya fitar da hayaki. Mataimakin Shugaban Kasa a lokacin Namadi Sambo yace hayakin nan babban illa ne ga lafiyar al’umma.

An gano rishon Biliyan 9 da Jonathan ya saya bayan shekaru 3
Jonathan ya bada kwangilar risho na Biliyan 9 a 2015

Sai dai mun ji cewa shekaru 3 da yin wannan alkawari rishon ba su je hannun matan da aka ce ba. Asali ma dai rishon na nan jibge a filin wasan Najeriya da ke Abuja, wasu kuma na nan an ajiye a wani gidan wasan yara a Birnin Tarayyar.

KU KARANTA: Wani Bature da ke taimakon Musulmai ya rasu

Idan ba ku manta ba a wancan lokacin dai Ma’aikatar muhalli ta bayyana cewa ba a gama biyan kudin kwangilar ba. Daga baya dai kurum sai aka ji cewa Gwamnatin Tarayya ta dakatar da wannan shiri bayan an yi wa jama’a alkawari.

Wata Jami’ar Ma’aikatar tace Gwamnati ta saki Biliyan 5 domin sayo rishon amma Biliyan 1.3 kurum aka ba ‘Dan kwangilar domin ya gaza cika alkawarin da yayi. Daga baya dai an shiga Kotu da Gwamnatin Najeriya kan saba yarjejeniyar.

Yanzu haka dai bayan kashe makudan kudi wadannan kayan girki su na ajiye a wulakance sun ma kama hanyar lalacewa. Gwamnatin Buhari dai har yau ba tace komai ba game da wannan kwangila.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng