2019: EFCC ta bukaci bankuna da su gabatar da sunayen barayi

2019: EFCC ta bukaci bankuna da su gabatar da sunayen barayi

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Ibrahim Magu ya bukaci bankuna da su samar da sunayen barayin abokan ciniki kafin zaben 2019.

Wata sanarwa daga kakakin hukumar EFCC, Mista Wilson Uwujaren ya bayyana cewa Magu ya sanar da hakan a ranar Talata a jihar Lagas yayin tattaunawa da kungiyar manyan jami’’ai na bankunan Najeriya.

Shugaban na EFCC yace hakan zai taimaka wajen rage yawan cin hanci da rashawa a kasar, inda ya kara da cewa bankuna da daman a kokarin durkushewa a yanzu sakamakon ayyukan barayin mutane.

2019: EFCC ta bukaci bankuna da su gabatar da sunayen barayi
2019: EFCC ta bukaci bankuna da su gabatar da sunayen barayi

Ya kuma umurci bankuna da su dunga ba hukumar bayanai day a kamata domin taimaka masu wajen aiwatar da ayyukan da rataya a wuyansu.

KU KARANTA KUMA: Komawa APC ba zai cece ku ba – Fadar shugaban kasa tayi ba’a ga barayin yan siyasa

Magu ya kuma nuna damuwa akan asusu masu zaman kansu a Najeriya, inda yace yan siyasa na iya sheganta damar.

Daga karshe Magu ya bayyana cewa hukumar a shirye take ta taimakawa bankuna wajen dawo da gurbatattun basusukka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel