Tace gaskiya ko zuqi-ta-malle cikin jawaban shugaban kasa a May 29th

Tace gaskiya ko zuqi-ta-malle cikin jawaban shugaban kasa a May 29th

- Anyi bikin dimokuradiyya a Mayu 29 watau jiya

- Shugaban kasa ya saki jawabinsa na ayyukan da yayi

- Tace gaskiya ko zuki ta malle a cikin jawaban

Tace gaskiya ko akasinta cikin jawaban shugaban kasa a jiya
Tace gaskiya ko akasinta cikin jawaban shugaban kasa a jiya

Wata kungiya mai kokarin tace gaskiya da rarrabe ta da karya ko zuki-ta mallen 'yan siyasa ta karyata akalla bakwai daga cikin manyan batuutwa da shugaban kasa Janar mai Ritaya Muhammadu Buhari ya wallafa a jiya.

A cewar kungiyar, Africa Check, wasu abubuwan dai duk kawai siyasa ce da romon baka irin na 'yan siyasa amma babu gaskiya cikinsu, ga dai wadanda suka zayyana cewa ba haka batun yake ba:

DUBA WANNAN: Guguwa tayi barna a Kebbi

1. Fadin cewa an ware 30% daga kasafin kudi na bana don manyan ayyuka wanda a baya ba'a taba yi ba; Karya ne, inji kungiyar, domin tun 2008 akalla sau uku ana zarta 30%. A 2008, 2010 da 2013.

2. Batun gyara tattalin arziki fiye da gwamnatocin baya, nan ma tace hauhawar farashi nha nuna shaci fadin APC ne kawai shugaba Buhari ya karanto.

3. Sai batun samar da wutar lantarki, nan ma sunce ba'a yanko daidai ba, inda shugaban ke cewa sun samar da Megawatt har 7,500 ya zuwa yanzu. Wai ai a kididdiga 105,152 MWh/h (4,381 MW), kadai aka iya samu mafi girma a a disambar bara watau 2017.

Sunyi alkawarin kawo sauran nan gaba...

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel