Bahaushe mai ban haushi: Uwargida ta maka Uban ýaýanta gaban Kotu kan watsi da yaransu

Bahaushe mai ban haushi: Uwargida ta maka Uban ýaýanta gaban Kotu kan watsi da yaransu

Wata Mata mai suna Hajara Muhammad ta shigar da karar Abdulkadir Muhammad gaban Kotun shariar Musulunci dake unguwar Magajin Gari a jihar Kaduna kan rashin biyan kudin makarantar yaran da rashin ciyar dasu da tace mijin nata ba yayi.

Hajara ta bayyana ma Kotun cewa tsohon Mijinta nata ya kasa sauke nauyin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na Uba ga yayansu guda uku, inda tace tun bayan shekaru hudu da suka rabu baya tabuka ma yayansa komai.

KU KARANTA: Babu abinda suka fi razana ni game da zaben 2019 kamar abubuwa guda 2 – Inji Jega

Uwargida ta shaida cewa itace take daukan dawainiyar yayan nasu, don haka ta roki Kotu ta tilasta masa biyan kudin makarantar yaran tare da daukan dawainiyarsu gaba daya, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito ta.

Sai dai shi ma mahaifin yaran, Abdulkadir ya tabbatar da gazawarsa wajen sauke nauyin da ya rataya akansa, inda yace halin matsin tattalin arziki da ake ciki ne ya sanya shi kasa daukan nauyin yayansa, daga nan sai ya roki Kotu ta yi masa alfarma ya dinga biyan matar naira dubu goma duk wata don ciyar da yaran da biya musu kudin makaranta.

Bayan sauraron bangarorin biyu, Alkalin Kotun, Mai Sharia Dahiru Lawal ya tabbatar ma Abdulkadir hakkinsa na kula da dawainiyar yayansa, sa’nnan ya bayyana cewa dole ne miji ya nemi kudi ya biya ma iyalansa bukata, daga karshe kuma ya umarce shi ya tabbata yay a dinga biyan tsohuwar matarsa kudi N10,000 a duk wata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel