Babban magana: Ana barazanar kashe golan Liverpool saboda wasan Madrid

Babban magana: Ana barazanar kashe golan Liverpool saboda wasan Madrid

Rahotanni sun kawo cewa 'Yan sandan Merseyside sun bayyana cewa suna sane da sakonnin barazanar kisa da ake turawa golan Liverpool Loris Karius bayan wasan karshe na gasar zakarun Turai.

Ana ta turawa dan kwallon na kasar Jamus, mai shekara 24, da iyalansa sakonnin barazana bayan kuskure biyu da ya yi wanda ya taimaka wa Real Madrid wajen doke su da ci 3-1 a wasan da aka gabatar a ranar Asabar, 26 ga watan Mayu.

Karius ya barke da kuka bayan an tashi daga wasan sannan kuma ya nemi afuwar magoya baya.

Babban magana: Ana barazanar kashe golan Liverpool saboda wasan Madrid
Babban magana: Ana barazanar kashe golan Liverpool saboda wasan Madrid

Dan wasan ne ya bai wa Karim Benzema kwallon farko da ya ci cikin sauki.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shehu Sani ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamna a jihar Kaduna

Daga bisani Karius ya kasa tare kwallon da Gareth Bale ya buga daga nesa wacce ta bai wa Madrid damar saka kwallo ta uku da kuma lashe kofin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng